Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

30 Mayu 2021

13:19:00
1145863

An Gudanar Da Gagarumar Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Palasdinawa A Birnin Washington Na Kasar Amurka

Masu Zanga-zangar sun rika bayar da taken yin tir da laifukan yakin da HKI ta tafka akan al’ummar Palasdinu, sannan kuma su ka bukaci gwamnatin Amurka da ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa HK ta yahudawa.

ABNA24 : Kwanaki biyu da suka gabata, kungiyar ma’aikatan tashoshin ruwa ta California ta yi tir da hare-haren na Isra’ila akan fararen hula Palasdinawa. Bugu da kari kungiyoyi fafutuka sun yi nasarar hana wani jirgin ruwan Amurka tsayawa a a tashar jirgin ruwa ta Okland dake Carlifonia.

Palasdinawa masu yawa ne dai su ka yi shahada sanadiyyar hare-haren na HKI, a yankin Gaza, daga cikinsu hadda kananan yara 66 da mata 39.

342/