Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : parstoday
Jummaʼa

28 Mayu 2021

14:21:51
1145152

An Kai Hari Akan Ayarin Motocin Sojan Amurka A Iraki

Majiyar tsaro daga kasar Iraki ta ce an kai hari akan ayarin da ke dauke da kayan aiki na sojojin Amurka a yankin kudancin kasar.

ABNA24 : Kafar watsa labaru ta Saberin ta ce; An kai harin ne dai a gundumar al-Samawah da ke kudancin kasar.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai hari, kuma babu wani rahoto cewa an sami asara ta rayuka ko ta dukiya.

A cikin watannin bayan nan dai ana tsananta kai hare-hare akan ayarin sojojin Amurka a kudancin kasar ta IRaki,.

A ranar Larabar da ta gabata ma dai an kai wani hari kwatankwacin wannan da abubuwan masu fashewa akan ayarin sojan na Amurka.

Tun bayan kisan gillar da Amurka ta yi wa shahid Kassim Sulaimani da Abu Mahadi al-Muhandis, a watan janairu na shekarar da ta gabata kiyayya da Amurka yake karuwa a cikin kasar.

342/