Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

25 Mayu 2021

12:50:03
1144225

Abinda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Je Yi A Gabas Ta Tsakiya

Sakataron harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya fara wata ziyara a gabas ta tsakiya, inda zai ziyarci Isra’ila da yankunan Falasdinawa da Masar da kuma Jodan.

ABNA24 : Ziyarar tasa wacce ita ce irinta ta farko a yankin, na zuwa ne kwana hudu bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.

Wani jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa ziyarar na da nufin karfafa yarjeejniyar tsagaita wutar da aka cimma bayan shafe kwanaki 12 na rikici tsakanin bangarorin biyu.

Kuma a game da hakan sakataren harkokin wajen Amurkar zai gana da dukkan bangarorin dake da ruwa da tsaki game da yarjejeniyar, amma banda kungiyar Hamas, dake da iko da Zirin Gaza wacce Amurkar ke kallon a matsayin ta ‘yan ta’adda.

An bayyana cewa, yayin da ake sa ran Amurka za ta kara bayyana goyan bayan ta ga Isra’ila akan abunda ya shafi kare kanta, za ta kuma jadadda bukatar samar da kasashe biyu Falasdinu da kuma Isra’ila a matsayin mafit agame da kawo karshen rikicin bangarorin biyu, sabanin tsohuwar gwamnatin Donald Trump, dake fifita Isra’ila akan Falasdinawa.

342/