Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

20 Mayu 2021

14:14:08
1142825

Amurka:Wasu ‘Yan Majalisar Wakilan Amurka Sun Gabatar Da Doka Ta Hana Amurka Sayarwa Isra’ila Makamai

Wasu ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Alexandria Ocasio suna gabatar da bukatar kafa wata doka wacce zata hana gwamnatin AMurka sayarwa haramtaccyar kasar Isra’ila makamai wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon 735.

ABNA24 : Jaridar POLITICO ta kasar Amurka ta nakalto majiya majalisar tana fadar haka, ta kuma kara da cewa Alexandria tare da wasu yan majal;isar wadanda ska hada da Elham Umar da Rashida Tlaib, Mark Pocan da kuma wasu da dama suna daga cikin wadanda suka gabatar da wannan bukatar.

Tun ranar 10 ga watan Mayun da muke ciki ne dai haramtacciyar kasar Isra’ila ta fara kai hare-hare babu kakkautawa kan al-ummar Falasdinu a yankin Gaza, inda suka yi ta kashe fararen huta da kuma rusa gidajen mutane a kansu dare da rana.

Arin mummunan ta’asar da HKi take aikatawa a yankin na Gaza ya tana hankalin mutane da dama duk fadin duniya, wanda kuma shi ya sa wadan nan yan majalisar wakilan Amurka suka bukaci a dakatar da sayarwa HKI makamai.

Amurka dai ita ce a gaban wajen sayarwa HKI makamai da kuma bata dukkan kariyar da take bukata don ta ci gaba da kashe al-ummar Falasdinu da kuma kwace gidajensu.

342/