Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

17 Mayu 2021

12:55:14
1141841

​Kwamitin Musulmin Amurka Ya Soke Taron Idi A Fadar White House Saboda Matsayar Biden A Kan Isra’ila

Kwamitin musulmin kasar Amurka ya sanar da soke taron idin karamar salla da aka shirya gudanarwa a yau a fadar White House saboda goyon bayan da Biden yake baiwa Isra’ila.

ABNA24 : Jaridar Politico ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kwamitin musulmin kasar ta Amurka ya fitar, ya bayyana cewa ba za su halarci taron idin karamar salla da aka shirya gudanarwa a fadar White House, saboda matsayar da gwamnatin Joe Biden ta dauka, wajen takawa Isra’ila burkia kisan kiyashin da take yi wa mata da kananan yara a Falastinu.

Babban sakataren kwamitin musulmin kasar ta Amurka Nahad Awad ya bayyana cewa, babban abin bakin ciki ne da takaici yadda shugaba Biden ya nuna halin ko in kulak an abin da yake faruwa na kisan gillar da Isra’ila take yi a zirin Gaza da sauran yankunan Falastinawa.

A kan haka ya ce sun yanke shawara a kan rashin halartar wannan taro, domin yin hakan na matsayin cin amanar al’ummar Falastinu ne, kuam hakan sabanin abin da aka yi zaton cewa Joe Biden zai aikata ne dangane da batun Falastinawa.

A ranar Juma’ar da ta gabata Joe Biden ya bayyana cewa, shi da maidakinsa sun kagara domin halartar taron idin karamar salla da za a shirya a fadar White House a ranar Lahadi tare da halartar musulmi daga sassa na Amurka, amma kuma ya san cewa abin da yake faruwa tsakanin Isra’ila ya saya dukkanin musulmi cikin bakin ciki da damuwa, kuam a cewarsa yana iyakacin kokarinsa domin ganin an dakatar da bude wuta.

342/