Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

16 Mayu 2021

17:59:55
1141568

​Amurka: Bernie Sanders Ya Caccaki Gwamnatin Netanyahu Kan Kisan Falastinawa

Dan majalisar dattijan Amurka Bernie Sanders ya yi tir da irin tsatsauran ra'ayin Netanyahu.

ABNA24 : A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, dan majalisar dattijan na Amurka Bernie Sanders ya bayyana cewa, irin matsananciyar akidar Netanyahu ce ta kara sanya lamurra suka tsanata a wanann lokaci da kowa ke son zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Ya ci gaba da cewa a kowace shekara gwamnatin Amurka tana ware dala biliyan 4 da take bai wa Isra'ila a matsayin taimako, ya ce bai kamata wanann taimakon ya zama karkashin gwamnati irin ta Netanyahu ba, dole ne Amurka ta canja salo.

Ya ce kamar yadda Isra'ila take da hakki ta kare kanta, haka nan kuma su ma Falastinawa suna da hakki na rayuwa kamar kowane dan adam, kuma rayuwarsu tana da muhimmanci kamar kowa.

Sanders ya ce, idan irin wannan siyasar ta neman tashin hankali da rashin son zaman lafiya ta Netanyahu ta ci gaba da tafiyar da Isra'ila, to kuwa hadarin da zai biyo bayan hakan zai shafi ita kanta Amurka, da dukkanin kasashen turai da kuma latin Amurka.

342/