Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

10 Mayu 2021

13:55:32
1139645

‘Yan Wasan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Deportivo Palestino Da Ke Kasar Chile Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Al’ummar Palasdinu

Kungiyar Kwallon Kafar Deportivo Palestino ta kasar Chile ta nuna goyin bayanta ga al’ummar Palasdinu da suke fuskantar hare-haren HKI a cikin kwanakin nan, ta hanyar daura kyallayen nan na Palasdinawa da ake kira; Kufiyah.

ABNA24 : A shekarun baya ma dai wannan kungiyar ta kwallon kafa ta sanya taswirar Palasdinu a jikin rigunan wasa na dukkanin ‘yan wasanta, lamarin da ya fusata yahuwada ‘yan cirani a kasar. Sai dai duk da matsin lambar da yahudawan su ka yi, bai sa kungiyar ta cire taswirar ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Deportivo Palestino ta taba zama gwarzuwa a kasar ta Chine ta hanyar cinye kofin zakarun kasar sau biyu a 1955 da kuma 1978.

342/