Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

9 Mayu 2021

14:07:35
1139270

Kaso 44 Na Al’ummar Duniya Na Kallon Amurka A Matsayin Barazana

Wani nazari da aka gudanar a kasashe 53 ya gano cewa, kaso 44 na mutane a fadin duniya na kallon Amurka a matsayin barazana ga tsarin demokradiyya.

ABNA24 : A cewar nazarin, cikin mutane 53,000 da aka nazarta a kasashe 53, kaso 44 na ganin tasirin Amurka a kasashensu a matsayin barazana ga demokradiyya.

Cibiyar bincike ta Latana da hadin gwiwar cibiyar inganta demokradiyya ta Alliance of Democracies, wadda tsohon sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen ya kafa a Denmark ne suka gudanar da nazarin.

Baya ga wannan, nazarin ya nuna cewa, kaso 64 na mutane a fadin duniya na ganin rashin daidaiton tattalin arziki a matsayin barazana ga demokradiyya, inda kaso 53 ke ganin takaita ‘yancin fadar albarkacin baki a matsayin barazanar, yayin da wasu kaso 49 ke alakanta magudin zabe da barazanar.

Kana wasu kaso 48 kuma, na ganin manyan kamfanonin fasaha da galibinsu ke zaune a Amurka, a matsayin masu barazana ga tsarin demokradiyya.

342/