Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

3 Mayu 2021

13:45:03
1137393

Amurka Za Ta Saki Kudaden Iran Da Take Rike Da Su Da Su Ka Kai ِDala Biliyan 7

Tashar talabijin din al’mayadeen dake watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ce ta bayar da labarin da ke cewa; Mai yiyuwa ne Amurkan ta mayar wa da Iran din kudaden nata da sun kai dalar Amurka biliyan 7.

ABNA24 : Har ila yau tashar ta al-mayadeen din ta kara da cewa; Kasashen biyu suna shirin musayar fursunoni da su ka kunshi ‘yan leken asirin Amurka 4 da Iran take rike da su.

A lokacin gwamnatin Barrack Obama Iran ta sake wani dan leken asirin Amurka mai suna Jason Rezaian, bayan da Amurkan ta saki kudaden Iran da take rike da su a wancan lokacin da su ka kai dala biliyan daya da miliyan dari bakwai.

342/