Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

29 Afirilu 2021

14:09:09
1136166

Sakataren Wajen Amurka Ya Tattaunawa Ta Bidiyo Da Shugabannin Nigeria Da Kenya

Sakataren harkokin wajen na Amurka Antony Blinken ya ja kunnen shugabannin Afirka da su yi dari-dari da da abinda ya kira; karuwar rawar da China take takawa a cikin nahiyar, tare da yin alkawalin cewa Amurka za ta bunkasa mu’amalarta da kasashen Nigeria da Kenya.

ABNA24 : Sakataren harkokin wajen na Amurka ya kara da cewa: Ba wai muna bukatar wani ya zabi tsakanin yin hulda da Amurka ko China ba ne, amma dai ina bukatarku ku yi tunani mai zurfi.”

Bugu da kari Blinken ya kira yi ‘yan Afirka da su zabi abinda ya fi zama mafi dacewa ga kasashensu.

A nashi gefen, shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya gode wa sakataren harkokin wajen na Amurka akan yadda kasarsa ta yi sassauci akan matakan da gwamnatin Donald Trump ta dauka na tsananta izinin shiga cikin kasar.

Shugaban na Nigeria ya kuma yi alkawalin bunkasa alakar tsaro da Amurka dangane da yankunan da ake fama da rikice-rikice da su ka hada da Sahel.

342/