Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

28 Afirilu 2021

13:15:23
1135835

Boma-Bomai Sun Tashi Kan Hanyar Tawagar Sojojin Amurka A Iraki

Wasu kakafen yada labarai na kasar Iraki sun bayyana cewa wasu boma-bomai wadanda aka kera da hannu sun tashi a kan hanyar tawagar motocin sojojin Amurka a kan babban titin Zee-qaar daga kudancin kasar, wanda ya lalata wata mota daga cikin motocin tawagar dauke da kayakin yaki.

ABNA24 : Labarin ya kara da cewa mita 300 kacal tsakanin inda bom din na farko ya tashi da kuma na biyu. Kamfanin dillancin labaran Shafaq-News na kasar t Iraki ya bayyana cewa a garin Basra ma a kudancin kasar, wani bom din ya tashi a cikin tawagar sojojin mamaya na kasar ta Amurka a Iraki.

Tun shekarar da ta gabata ce majalisar dokokin kasar Iraki ta kafa dokar korar sojojin kasashen waje daga kasar Iraki, amma gwamnatin Amurka ta ki fidda sojojinta kimani 2,500 daga kasar.

342/