Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

26 Afirilu 2021

12:59:47
1135130

​Amurka Tana Kokarin Farfado Da Kungiyar Daesh A Kasar Iraqi

Mataimakin shugaban dakarun Nujabaa na kasar Iraki ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta na son farfado da kungiyar Daesh a kasar, ya ce shugaban kasar Amurka Joe Biden ya na da wannan manufar a kasar ta Iraki.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran ‘FuratNews’ ya nakalto Nasrul Ashamari ya na fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa dole ne dukkan dakaru da kuma jami’an tsaron kasar Iraki su shiga cikin aikin kakkabo ragowar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraki kuma dole ne su dauki matakan hana sake dawowar kungiyar a kasar.

Har’ila yau Mahmood Arrabi’i mamba a bangaren siyasa na dakarun Asa’ibu Ahlul Hak na kasar ta Iraki ya ce sojojin Amurka suna goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraki, don haka ficewar sojojin Amurka da ga kasar ne kawai zai kawo kungiyar a kasar.

Daga karshe labarin ya nakalto Hadi Al-Amuri shugaban gamayyar jam’iyyu ta ‘Fath’ ya na cewa dole sojojin Amurka su kawo karshen mamayar da sukewa kasar Iraki. Ya ce babu wani dalilin da zai sa sojojin Amurka su ci gaba da zama a kasar.

342/