Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

22 Afirilu 2021

13:45:47
1133989

​Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Maraba Da Tabbatar Da Laifi Kan Makashin George Floyd

Kotun Amurka ta samu Derek Chauvin da laifin kashe bakar fatar nan George Floyd a shari’ar da aka yi masa sakamakon shakare shi da ya yi.

ABNA24 : Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun kwashe sa’o'i 11 suna tafka mahawara a tsakaninsu kafin cimma matsayar cewar, Chauvin ya aikata laifuka guda 3 da aka tuhume shi akai da suka hada da kisan kai ba tare da niyya ba da kuma makure George Floyd har sai da ya daina numfashi.

Wannan matsayi ya haifar da murna daga mutanen da suka taru a harabar kotun da kuma wasu sassan Amurka, yayin da wasu suka zubda hawaye saboda farin ciki kan yadda shari’ar ta kaya, musamman lokacin da alkali Peter Cahill ke karanata ta, kafin daga bisani 'yan sanda suka maka wa Chauvin ankwa suka fitar da shi daga kotun.

Ana sa ran kotun za ta bayyana hukuncin daurin akalla shekaru 40 a gidan yari kan wanda aka asamu da laifin.

A nata bangaren majalisar dinkin dinkin duniya ta bayyana tabbatar da laifin kisa a kan mutumin da ya kashe George Floyd da cewa hakan abin farin ciki ne, kuma hakan shi ne adalci, amma duk da haka akwai sauran aiki dangane da irin wadannan matakai na rashin 'yan adamtaka da ‘yan sanda suke aikatawa a Amurka, abin da ya faru a cikin ‘yan kwanakin nan na kashe wani matashi bakar fata a hannun jami’an ‘yan sanda yana kara tabbatar da hakan.

342/