Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

20 Afirilu 2021

14:56:53
1133321

​Jirgin Yakin Rasha Ya Hana Wasu Jiragen Yakin Amurka Da Norway Kusantar Iyakokin Rasha Na Ruwa

Wani jirgin yakin rundunar sojin kasar Rasha ya hana wasu jiragen yaki biyu na Amurka da Norway kusantar iyakokin ruwa na kasar Rasha a cikin tekun Barents.

ABNA24 : A cikin wani rahoton tashar Russia Today, ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta fitar da wani bayani da ke cewa, na’urorin radar rundunar sojin ruwa ta kasar Rasha sun hango jirage biyu suna tunkarar iyakokin Rasha na ruwa a cikin tekun Barents.

Bayanin ya ce, bayan gano hakan, wani jirgin yakin rundunar sojin kasar Rasha ya taso daga cikin wani katafaren jirgin ruwa da ke dauke da jiragen yaki a arewacin kasar ta Rasha, inda ya tunkari jiragen biyu, kuam ya tilasta su sauya hanya.

Ma’aikatar tsaron ta Rasha ta bayyana cewa, jiragen biyu na Amurka da Norway suna daga cikin jiragen da ke sintiria cikin tekun, amma ba su da izinin tunkarar iyakokin ruwa na kasar Rasha.

342/