Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

18 Afirilu 2021

13:50:31
1132675

​Hukumar IAEA Ta Tabbatar da Cewa Iran Ta Fara Tace Sinadarin Yuranium Har Zuwa Kashi 60%

Hukumar IAEA mai kula da al-amuran sarrafa makamashin nukliya a duniya, wacce take karkashin MDD ta tabbatar da cewa kasar Iran ta fara tace sinadarin yuranium har zuwa kasha 60%, wanda ya tabbatar da ikrarin jami’an gwamnatin kasar.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta kara da cewa hukumar ta IAEA ta bayyana cewa, a ranar jumma’a mizanin gwajin ya kai kashin 55.3%. Kafin haka shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa hukumarsa ta fara wannan aikin a cibiyar tace sinadarin yuranium da ke Natanz.

Daga baya shugaban kasar ta Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa Iran zata tsaida aikin tashe sinadarin yuranim zuwa kashi 20% da 60% ne kawai idan Amurka ta koma cikin yarjejeniyar JCPOA sannan ta dagewa kasar dukkan takunkuman da ta dorawa kasar.

342/