Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

18 Afirilu 2021

13:49:23
1132674

Castro Ya Sanar Da Murabus Ɗinsa Daga Shugabancin Jam’iyyar Kwaminisanci Ta Cuba

Tsohon shugaban ƙasar Cuba, Raul Castro, ya sanar da murabus ɗinsa daga shugabancin jam’iyyar Kwaminisanci mai mulki a ƙasar, muƙami mafi girman matsayi a ƙasar.

Raul Castro ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da yayi a ranar farko ta taron ƙasa na jam’iyyar inda ya ce yana miƙa mulkin ne ga sabbin jini waɗanda suke da cikakken ƙumaji da kuma ruhin ƙiyayya da mulkin mallaka.

Har ila yau tsohon shugaban Cuban ya ce yin murabus ɗin nasa ba yana nufin shi kenan ya koma gefe ba ne, ya ce a shirye ya ke a koda yaushe matuƙar dai yana raye ya ci gaba da ba da tasa gudummawar wajen kare ƙasar, juyin juya halin da kuma tsarin gurguzu na ƙasar.

A jibi Litinin 19 ga watan Aprilu, wato ranar ƙarshe na taron, ne ake sa ran zai sauka daga wannan matsayin nasa inda za a zaɓi sabbin shugabannin jam’iyyar.

342/