Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

17 Afirilu 2021

12:42:23
1132334

Amurka Ta Kai Jiragen Yakin Samfurin F-16 Zuwa Kasar Saudiya Duk Da Cewa Tana Aibata Saudia A Yakin Da Ta Ke Yi A Kasar Yemen

Gwamnatin kasar Amurka ta aike da matuka jiragen yaki 300 da jiragen yaki da dama samfurin F-16 zuwa sansanin sojojin sama na Yerima Sultan a kasar Saudiya.

ABNA24 : Tahsar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mujallad ‘Air Force Magazin’ ta kasar Amurka ta na bada wannan labarin. Ta kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi haka ne don taimakawa kawayenta a yankin tekun farisa a duk lokacinda suke bukatar taimako.

Duk da cewa gwamnatin shugaba Biden a fili ta na cewa ba ta son yakin da Saudiya take jagoranta a Yemen, amma kuma a dayan bangaren, da makamanta ne kasar ta Saudia da kawayenta suke yaki a kasar ta Yemen.

Kafin haka gwamnatin Biden ta amince da cinikin jiragen yaki samfurin F-35 guda 50 ga kasar UAE a makon da ya gabata.

342/