ABNA24 : Fadar gwamnatin Amurkar ta ce nan gaba a yau Laraba Shugaba Biden, zai sanar da yadda za a kwashe dakarun a mataki-mataki.
Amurka dai ta kwashe shekara ashirin tana yaki a Afgasnitan, tun bayan tagwayen hare haren 11 ga watan Satumban 2001.
A watan Mayu wannan shekara ne ya kamata a ce sojojin na Amurka sun fice daga Afganistan kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma da ‘yan Taliban a Qatar lokacin mulkin tsohon shugaba Donald Trump ta tanada.
Saidai daga bisani sabon shugaban Amurka Joe Biden, ya ce da wuya sojojin na Amurka su fice a wannan lokacin.
A kwanan baya dai Kungiyar Taliban ta gargadi Amurka akan girbar abunda zai biyo bayan idan ta kasa kwashe sojojin nata kamar yadda yarjejeniyar ta Doha ta tanada.
342/