Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

15 Afirilu 2021

14:24:54
1131750

Sabuwar Gwamnatin Amurka Ta Ci Gaba Da Shirin Seyarwa UAE Makamai Na Kimanin Dalar Amurka Biliyon $23

Gwamnatin shugaban Amurka mai ci, ta ci gaba da shirin sayarwan kasar Hadaddiyar daular Larabawa ko (UAE) makamai wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka billiyon $23.

ABNA24 : Tashar talabjinin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tsohuwar gwamnatin Amurka ce ta amince da cinikin, awa guda kafin a rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka.

Makaman dai sun hada da jiragen yaki samfurin F-35 guda 50 da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa samfuran MQ-9B guda 18 da kuma wasu na’urori wadanda ake amfani da su a yake-yaken kayakan lantarki.

Bayan karbar ragamar shugabancin kasar a ranar 20 ga watan Jenerun wannan shekara dai Shugaban Biden ya dakatar da cinikin don gudanar da bincike, amma a halin yanzu ta tabbata cewa za’a ci gaba da cininki, inda ake saran UAE za ta karbi dukkan wadannan makamai nan da shekara 2025.

342/