Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

15 Afirilu 2021

14:18:09
1131743

Jagora : Ba Zamu Dawwama Ba Kullun Kan Tattaunawa Game Da Yarjejeniyar Nukiliya

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bukaci da kada a ja dogon lokaci a tattaunawar dake gudana da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015.

ABNA24 : Ayatollah Khamenei, ya kuma jadada cewa, Iran ba zata dakatar da matakan da take dauka ba game da yarjejeniyar har sai ta gani a zahiri, cewa Amurka, ta dage ma ta gabadayen takunkuman data kakaba.

Jagoran ya fada a jiya Laraba cewa, ya baiwa jami’an diflomatsiyan Iran umarnin su ci gaba da tattaunawa, amma tare sanin cewa ba za’a dawwama har kulun ba kan tattaunawa.

‘’ba za’a dawwama kan tattaunawa ba har illah masha Allahu, a cewar jagoran, don kada hakan ya zama wata hanya da sauren bangarorin da ke cikin yarjejeniyar zasu amfana da ita domin tsawaita yarjejeniyar ko da yaushe.

Kallaman na jagoran juyin juya halin musulincin na Iran, na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar Iran, da karamin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ke jagoranta ta isa a birnin Vienna na kasar Austrea, domin ci gaba da tattaunawa da sauren bangarorin dake cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, da suka da Biritaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, a wani mataki na lalubo hanyar da Amurka zata koma cikin yarjejeniyar da tsohon shugaba Donald Trump, ya janye Amurka data ciki a 2018, da kuma yadda za’a dagewa Iran jerin takunkuman da aka kakaba mata.

342/