Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

13 Afirilu 2021

12:49:38
1131118

Amurka : Ana Bore Bayan Dan Sanda Ya Bindige Wani Bakar Fata

Shugaba Joe Biden na AMurka ya bukaci a kai zuciya nesa, bayan zana zangar data barke a kasar bayan sake kisan wani bakar fada da dan sanda ya yi.

ABNA24 : Zanga-zanga ta barke a birnin Minneapolis bayan da wani dan sanda ya bindige wani matashi bakar fata har lahira.

Jim kadan bayan aukuwar lamarin, daruruwan mutane ne suka yi dandazo a gaban ginin babban ofishin ‘yan sandan garin Brooklyn Center dake birnin Minneapolis a jihar Minnesota, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaro harbawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa.

Lamarin na zuwa a daidai lokacin da ake shari’ar dan sandan da ake tuhuma da halaka wani bakar fata George Floyd a dai birnin na Minneapolis.

A ranar Lahadi ne dan sandan ya harbe, Daunte Wright matashin bakar fata mai shekaru 20 da bindiga.

342/