ABNA24 : Ministan harkokin wajen Amurka Antony J. Blinken ya ayyana nau’in takunkumin da ya zama wajibi a kakaba wa kamfanonin da suke kera wa Turkiya makaman tsaro da kuma sugabansu Isma’ila Dimir da wasu manyan jami’an kasar uku.
An kuma yi kira ga Amurkawa da kada su yi mu’amala da Turkawan da aka kakaba wa takunkumi, kamar kuma yadda za a rika kudaden ajiyarsu a cikin Amurka da hana su izinin shiga cikin kasar.
Bugu da kari Amurka za ta dakatar da sayen duk wasu kaya masu alaka da harkar tsaro da aka kera a kasar ta Turkiya.
342/