Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

5 Afirilu 2021

08:29:59
1128854

Amurka Ta Nada Rob Malley A Matsayin Shugaban Tawagarta Dangane Da Tarurrukan JCPOA

Tashar talabijin ta CNN ta bada sanarwan cewa wani babban jami’in gwamnatin Amurka mai suna Rob Malley zai jagoranci tawagar kasar a tarurruka na yarjejeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar Iran a birnin Vienna.

ABNA24 : Kafin haka dai shafin labarai na Axion ya bada labari a ranar Jumma’a kan cewa Malley ba zai halarci taron JCPOA na gaba wanda za’a gudanar a birnin Vienna a cikin mako mai zuwa ba.

A ranar jumma’an da ta gabata cewa aka gudanar da taron yarjejeniyar na 18 ta shafukan yanar gizo inda wakilan kasashe da kungiyoyin da yarjejeniyar ta shafa suka tattauna matsalolin da ficewar Amurka daga yarjejeniyar ya haddasa, da kuma hanyoyin dawowarta cikin yarjejeniyar.

Gwamnatin kasar Iran dai ta fara yin watsi da yerjejeniyar shekaru biyu bayan ficewra Amurka daga cikita, sannan ta ce ba zata koma kan kan yarjejeniyar ba sai idan Amurka ta dage dukkan takunkuman da ta dora mata bayan ficewaarta a shekara ta 2018.

342/