Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

4 Afirilu 2021

07:12:53
1128530

Amurka Ta Dauke Takunkuman Da Gwamnatin Trump Ta Dorawa Jami’an Kotun ICC

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan soke takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin da ta shude ta dorawa wasu daga cikin jami’an kotun kasa da kasa mai hukunta manya-manyan laifuffuka ta ICC.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana cewa shugaba Joe Biden ya soke takunkumi mai lamba 13928 wanda ya bukaci a toshe asusun ajiya da kuma na kadarorin wasu jami’an kotun ICC, daga cikinsu har da mai gabatar da kara na kotun Fatou Bensouda.

Kafin haka tsohon shugana kasar Amurkan Donal Trump ya sanyawa Bensoudeh takunkuman ne bayan da ta gabatar da shawarar bincike da kuma hukunta wadanda suke da hannun a laifuffukan yaki da cin zarafin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

Tuni dai kutun ta amince da aikin fara bincike a kan yahudawan Haramtacciyar kasar Israela wadanda suke da hannu a laifuffukan yake a kasar ta Falasdinawa.

342/