Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

30 Maris 2021

18:32:23
1127678

Brazil : Ministan Harkokin Waje Da Na Tsaro Sun Yi Murabus

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro, ya yi gagarumin garanbawul a majalisar ministocinsa, sakamakon murabus din da ministan harkokin waje da kuma na tsaro na kasar suka yi, a jere.

ABNA24 : Murabus din jam’an biyu babban koma baya ne ga shugaban kasar Jair Bolsonaro, dake shan suka wajen kasa shawo kan al’amarin annobar korona a kasar.

Wannan gibi da aka samu kwatsam a gwamnatin, ya bude kofar, gagarumin gyaran fuska a tafiyar, inda Shugaba Bolsonaron ya sauya ministoci shida.

Wannan koma baya da gwamnatin ta samu, na zuwa ne bayan sake bullowar babban abokin hamayyar shugaba Bolsonaro, tsohon shugaban kasar ta Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.

342/