Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

27 Maris 2021

13:18:24
1126944

Mabiya Sheikh Zakzaky Sun Gudanar Da Gangamin Neman A Sake Shi, Gabannin Sake Gurfanar Da Shi A Gaban Kotu

Rahotanni daga Abuja babban birnin Tarayyar Nijeriya sun bayyana cewar mabiya jagoran harkar Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun gudanar da wani gangami a babban masallacin Juma’a na ƙasa na birnin (National Mosque) inda suka buƙaci gwamnati da ta saki jagoran na su ba tare da wani sharaɗi ba.

ABNA24 : Rahotannin sun ce wani adadi mai yawa na mabiya Shehin malamin ne suka gudanar da wannan gangamin jim kaɗan bayan idar da sallar juma’a a jiya Juma’a inda suke ɗauke da hotunansa da kuma wasu ƙyallaye da suke buƙatar mahukuntan Nijeriyan da su saki malamin na su ba tare da wani sharaɗi ba.

Ɗaya ga cikin ƙyallayen da mabiya Sheikh Zakzakin suka ɗaga yana ɗāuke da rubuta da harshen turanci da ke cewa: We Demand For Unconditional Release of Sheikh Zakzaky (wato muna buƙatar da a saki Sheikh Zakzaky ba tare da wani sharaɗi ba).

Har ila yau mahalarta gagangani suna rera taken cewa shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya sake musu shugabansu, suna masu nuna cewa a shirye suke su mutu saboda jagoran na su.

Wannan gangamin dai yana zuwa ne ‘yan kwanaki kafin ci gaba da shari’ar da ake yi wa Sheikh Ibrahim Zakzaky a jihar Kaduna wanda za a gurfanar da shi a ranar 31 ga watan nan na Maris.

Idan dai ana iya tunawa a ranar 9 ga watan Maris ɗin nan ne dai aka sake gurfanar da Sheikh Zakzaky ɗin da mai ɗakinsa a gaban babban kotun jihar Kaduna bisa zargin kisan kai, taro ba bisa ƙa’ida ba, tada hankalin al’umma da dai sauransu, lamarin da Shehin malamin da mai ɗakin nasa suka musanta.

A zaman na ranar 9 ga watan dai masu shigar da ƙara sun ci gaba da gabatar da shaidunsu, inda daga ƙarshe dai alƙalin kotun mai shari’a Gideon Kurada ya ɗage sauraren ƙarar har sai zuwa ranar 31 ga watan Maris ɗin don ci gaba.

Ana ci gaba da tsare Sheikh Zakzaky da mai ɗakin nasa ne dai a gidan yarin Kaduna duk kuwa da rashin lafiyar da suke fama da shi, wanda wasu ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bil’adama musamman ƙungiyar nan ta IHRC suka nuna damuwarsu sosai dangane da halin da suke cikin.

342/