Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

25 Maris 2021

13:26:24
1126278

Amurka: Adadin Mutanen Da Su Ka Kamu Da Cutar Corona A Kasar Amurka Sun Haura Miliyan 30

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto cewa; Adaidai lokacin da ake gaggauta yin allurar rigakafin cutar Corona a kasar Amurka, adadin wadanda su ka kamu da ita sun haura miliyan talatin.

ABNA24 : Rahoton ya ci gaba da cewa; Alkalumma suna da nuni da cewa a kowane mako ana kara samun yawan wadanda suke kamuwa da cutar. Sai dai jihohin kasar ta Amurka suna rigegeniya da juna wajen ganin an yi mafi yawancin mutane allurar rigakafin.A jihohin da suka hada Alaska, Arizona, Texas an fara yi wa mutanen da shekaru suke kasa allurar rigakafin, bayan da aka faro ta daga kan masu manyan shekaru.

Sabanin nasihohin likitoci, wasu daga cikin jihohin na Amurka sun yi watsi da wajabcin daura takunkumin rufe baki, lamarin da ake ganin ya taka rawa wajen kara yaduwar cutar.

Ya zuwa yanzu adadin wadanda cutar ta kashe sun kai rabin dubu daribiyar da 44.

342/