Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

18 Maris 2021

14:36:20
1124519

Amurka Da Burtaniya Za Su Kara Inganta Makamansu Na Nukliya A Dai-dai Lokacinda Suke Hana Iran Amfani Da Nukliya Ta Zaman Lafiya

Gwamnatin kasar Amurka tana shirin sabonda kera makaman nukliyarta ta yadda zasu tafi da zamani. Tashar talabijin ta Presstv a nana Tehran ta nakalto ma’aikatar tsaron kasar Amurka Pentagon ta na fadar haka. Ta kuma kara da cewa za ta kashe dalar Amurka biliyon $100 don sabonta makamanta masu linzami wadanda kuma zasu iya daukar makaman nuliyar har zuwa tazarar kilomita 10,000 daga inda aka cillasu.

ABNA24 : Banda haka makaman masu linzami su na iya daukar makaman nukliya wadanda nauyinsu ya ninninka wadanda Amurkan ta jefa a kan kasar Japan a yakin duniya na biyu har sau 20. Har’ila yau firai ministan kasar Burtaniya Boris Johson ya bada sanarwan cewa kasarsa zata kara inganta makamatanta na nukliya da kashi 40% a karon farko tun bayan yakin duniya na biyu.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne don iran barazanar da ta ke fuskanta a bangarorin Rasha da China, Sannan ta ce za ta kara yawan sojojinta a kasashen waje don sanyasu cikin ayyukan ko ta kwana a ko ina a duniya.

Kungiyoyi masu yaki da hana yaduawar makaman kare dangi a duniya dai, duk sun yi allawadai da matakan da wadannan kasashe suke dauka, don hakan zai sa sauran kasashen duniya su fara gasar mallakan irin wadannan makaman.

342/