Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

17 Maris 2021

13:03:29
1124167

Rahoto : Amurka Ce Ta Fi Kowace Kasa Fitar Da Makamai Zuwa Ketare

Wani rahoto da wata cibiyar bincike dake Sweden, ta fitar ya nuna cewa, Amurka ce ke kan gaba wajen fitar da makamai zuwa ketare.

ABNA24 : Rahoton wanda cibiyar ta SIPRI, ta fitar a jiya Litinin ya ce, Amurka ta kasance kasar da ta fi kowace kasa a duniya fitar da makamai zuwa ketare, kana ta kara matsayinta na fitar da makamai daga kashi 32 bisa 100 a tsakanin shekarun 2011-2015 zuwa matakin kashi 37 bisa 100 tsakanin shekarun 2016-2020.

Cibiyar, ta bayyana cikin rahoton bincikenta na baya bayan nan cewa, kasar Amurka ta sayar da manyan makamai ga kasashe 96 tsakanin shekarun 2016-2020, sama da kowace kasa a duniya.

Kusan rabin adadin wato kashi 47 bisa 100 na makaman da Amurka ta fitar sun tafi ne zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasar Saudiyya kadai ta samu kashi 24 bisa 100 na yawan makaman da Amurkar ta fitar zuwa ketare.

Haka ma kasashen faransa da Jamus sun kara yawan makamman da suke sayar wa a yankin gabas ta tsakiyya.

Amma duk da hakan rahoton cibiyar ta SIPRI, ya ce an dan samu raguwar cinikin makamman yaki a cikin shekaru biyar na baya bayan nan, wanda shi ne karon farko tun farko wannan karni.

342/