Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

14 Maris 2021

14:06:12
1123328

​Iraki: Kungiyar Gwagwarmaya Ta ‘Ahlul Kahf’ Ta Dauki Alhakin Kaiwa Sojojin Amurka Hari A Kudancin Kasar

Kungiya ‘Ahlul Kahfi’ mai gwagwarmaya da mamayar da sojojin Iraki sukewa kasar Iraki ta dauki alhakin kai hare-haren da aka kaiwa tawagar sojojin Amurka a lardin Kadisiyya na kudancin kasar.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen a kasar Lebanon ta nakalto bayanin da kungiyar ta fitar a safiyar yau Asabar na cewa ita ce da alhakin tada nakiya a kan hanyar tawagar sojojin Amurka a lardin Kadisiyya na kudancin kasar. A cikin bayanin kungiyar ta yi kira ga Irakawa wadanda suke aiki da sojojin Amurka a kasar, da su nisanci sojojin na Amurka, idan bah aka ba su yi kuka da kansu bisa duk abinda ya samesu.

Har’ila yau kungiyar ta kammala da cewa za ta kai hare-hare a kan duk wata maslaha ta sojojin Amurka a kasar ta Iraki har zuwa lokacinda zasu fice daga kasarsu.

342/