Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

14 Maris 2021

14:03:46
1123326

​Gwamnatin Habasha Ta Musanta Zargin Amurka Na Cewa Tana Son Shafe Yan Kabilar Tigray

Gwamnatin kasar Habasha ta musanta zargin Amurka na cewa tana son shafe ‘yan kabilar Tigray a lardin Amhara na arewacin kasar.

ABNA24 : A wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha ta fitar a yau Asabar, ma’aikatar ta musanta zangin gwamnatin Amurka ta kuma kara da cewa wannan zargin ba gaskiya bane.

A ranar Laraban da ta gabace sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya zargi gwamnatin kasar ta Habasha da kokarin shafe yan kabilar Tigray a yankin Amhara na arewacin kasar a lokacinda ya ke amsa tambayoyi a majalisar dokokin kasar ta Amurka dangane da shirin shugaba Biden na harkokin waje.

A cikin watan Nuwamban da shekarar da ta gabata ce, sojojin kasar Habasha ta kwace iko da babban birnin Lardin Amhara Mekelle daga hannun jam’iyyar ‘Tigray People’s Liberation Front (TPLF) wacce ta ke iko da yankin.

Jami’an agaji na kasa da kasa sun zargi gwamnatin kasar Habasha da kashe fararen hula da kuma hana su isa cikin yankin don isar da abinci da magunguna ga mutanen yankin.

342/