Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

13 Maris 2021

13:57:28
1122992

MDD Ta Jinjinawa Majalissar Wakilan Libiya Bisa Amincewarsu Ta Kafa Sabuwar Gwamnati

Tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a Libiya ko UNSMIL a takaice, ta jinjinawa majalissar wakilan kasar, bisa amincewar ta a kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa.

ABNA24 : Mai magana da yawun majalissar Abdullah Balhig, ya ce, majalissar wakilan kasar ta mara baya ga wannan kuduri, da rinjayen kuri’u 132, bayan da majalissar sulhunta rikicin siyasar kasar ko LPDF, mai samun goyon bayan MDD ta zabi sabbin jagororin kasar, da goyon bayan daukacin sassan masu ruwa da tsaki.

Sabbin jagororin kasar ta Libya dai na da nauyin shirya manyan zabukan kasar dake tafe, a ranar 24 ga watan Disambar bana, kamar dai yadda majalissar sulhunta rikicin siyasar kasar ta LPDF ta amince da hakan.

342/