Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

10 Maris 2021

19:26:02
1122262

​Amurka: Wadanda Trump Ya Haramtawa Shiga Kasar Za Su Iya Sake Cika Takardun Neman Izinin Shiga

Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, wadanda aka hana shiga cikin kasar a baya a halin yanzu za su iya sake neman izinin shiga.

ABNA24 : Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka Ned Price ta bayyana cewa, wadanda aka hana shiga cikin kasar Amurka kafin 20 ga watan Janairun 2020, a halin yanzu za su iya sake neman izinin shiga kasar tare da biyan wasu kudin visa.

Haka nan kuma wadanda suka nemi izinin shiga kasar daga ranar 20 ga watan Janairun 2020 ko bayan hakan, za su iya bin kadun lamarin, ba tare da sun sake rubuta neman wani izinin shiga ko biyan wasu kudi ba.

Tun daga watan Disamban 2017, gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta sanar da kafa dokar shigar ‘yan wasu kasashe a cikin kasarta, da suka hada har da na musulmi.

Daga cikin kasashen akwai Myanmar, Iretrea, Iran, Somalia, Kirgystan, Libya, Najeriya, Koriya ta arewa, Sudan, Syria, Tanzania da kuma Venezuela.

Farkon aikin da Joe Biden ya fara yi a ranar 20 ga watan janairun wannan shekara da ya karbi mulkin Amurka, shi ne rusa wannan doka.

342/