Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

6 Maris 2021

08:23:41
1121040

Hukumar IAEA Ta Yi Watsi Da Batun Samar Da Sabon Kuduri Don Ladabtar Da Iran Saboda Kara Nisantar Yarjejeniyar JCPOA Da Ta Yi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bada labarin cewa hukumar IAEA ta dakatar da batun kuduri na ladabtar da Iran saboda kara nesa da ta yi daga yarjejeniyar JCPOA.

ABNA24 : Sa’id Khadib Zade ya bayyana haka ne a safiyar yau Alhamis ya kumam kara da cewa, hukumar ta dakatar da shirin nata ne bayan muhawara mai zafi tsakaninta da kasar Iran.

KhadibZadeh ya kara da cewa yin watsi da wannan shirin ya sake bude damar tattaunawa da kuma daukar hanyoyin diblomasiyya don kawo karshen takadda dake tsakanin Iran da kasashen tarayyar Turai da Amurka dangane da yadda kasashen zasu dabbaka yarjejeniyar JCPOA ta shirin nukliyar kasar Iran.

342/