Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

4 Janairu 2021

11:14:04
1103047

​Janar Kasim Sulaimani Ya Taka Gagarumar Rawa Wajen Tabbatar Da Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Wakilin Jihadul Islami a Tehran ya bayyana janar Kasim Sulamini da cewa shi ne ya taka wa kasashen yamma da yahudawa gami da ‘yan korensu burki a gabas ta tsakiya.

ABNA24 : A cikin bayaninsa a jiya wakilin Jihadul Islami ta Falastinu a Tehran ya bayyana cewa, ko shakka babu Kasim Sulamini ya bayar da gudunmawa a bangarori daban-daban ga al’ummomin yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce babbar gudunmawa da ya bayar ga al’ummar wannan yanki ko sun sani ko ba su sani ba, ita ce ya hana wa kasashen yammacin turai da yahudawan sahyuniya gami da ‘yan korensu na yankin gabas ta tsakiya burki a gabas ta tsakiya, kafa abin da suke kira sabuwar gabas ta tsakiya.

Ya ce baya ga haka kuma, al’ummar Falastinu sun san irin gudunmawar da ya bayar wajen hana yahudawan sahyuniya cimma burinsu na mamaye yankin zirin Gaza, inda bai taba gajiyawa ba wajen taimaka ma falastinawa ‘yan gwagwarmaya da makamai domin su kare kansu da kasarsu.

Haka kuma yakin Lebanon na shekara ta 2006, shi ne gishikin nasarar da aka samu kan yahudawa wajen murkushe kaidinsu a kan al’ummar Lebanon, kamar yadda ya bayar da gudunmawa wajen korar yahudawan Isra’ila a cikin shekara ta 2000 da suka mamaye kudancin Lebanon, inda suka fita babu shiri.

Baya ga haka kuma shi ne ya taka gagarumar rawa wajen karya lagon 'yan ta'addan takfir a Syria da Iraki da kuma Lebanon.

342/