Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

1 Janairu 2021

13:35:59
1101848

A Iran, yayin da ake tunkarar zagayowar ranar shahadar Janar Qassem Suleimani, shugaban kasar Hassan Rohani, ya bayyana cewa ba shakka shugaba Trump da Mike Pompeo ne kan bayan kisan da akayi wa janar din a kasar Iraki.

ABNA24 : Shugaba Ruhani, ya bayyana ce al’ummar Iran da kuma musulmin duniya ba zasu taba manta wa da jarimin Shahid Soleimani.

M. Rohani ya kuma danganta shahidin da abun alfahari da al’ummar Iran da kuma musulmin kasashen yankin ba zasu taba mantawa ba da shi ba.

Ya ce kisan Janar Soleimani, wata hanya ce da Amurka ta amfani da ita na fuce takaicin Iran, saboda kin mika kai ga makiya.

Iran dai a cewarsa ba zata taba mantawa ba da kisan, wanda kuma ‘yancin al’ummar Iran ne na su maida martani kan zubar jinin shahidin Qassem Sulaimani.

A ranar 3 ga watan Janairu na shekarar nan dake shirin karewa ne Janar Qassem Suleimani ya yi shahada a wani hari da shugaba Trump na Amurka ya bada umarinin kaiwa kan tawagar motocinsa lamarin da ya yi sanadin shahadarsa da shi da mambobin tawagar dake mara masa baya ciki har da Abu Mahdi Al Muhandis na Iraki.

342/