Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

30 Disamba 2020

16:47:26
1101196

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana cewa babban kuskure abunda Amurka ta yi na kisan Janar Qassem Sulaimani.

ABNA24 : Mista Zarif, ya bayyana hakan ne shafinsa na twitter, yayin da ake tunkarar zagayowar shekara guda da kisan da Amurkar bisa umarnin Donald Trump ta yi wa janar din Shahid Qassem Sulaimani.

Zarif, ya kuma ce kada kuri’ar da wakilan al’ummar Iran a majalisar dokoki kasar sukayi na kore dakarun Amurka, shi ne zai kawo karshen sojojin na Amurka a yankin.

A ranar 3 ga watan Janairu na shekara 2020 din nan ne Janar Ghassem Soleimani ya yi shahada a wani hari da Amurka ta kaiwa tawagar motocinsa a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki, bisa umarnin shugaba Trump.

Iran dai ta ce har yanzu tana kan bakarta na cewa zata dauki fansa akan kisan da akayi wa Janar din nata shahid Ghassem Soleimani.

342/