Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Talata

29 Disamba 2020

15:17:18
1100826

​Nasrallah: Qassem Sulaimani Ya Bayar Da Gudunmawa Wajen Tabbatar Da Tsaron Gabas Ta Tsakiya

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, gwamnatocin Amurka, Isra’ila da Saudiyya ne suka kashe Qassem Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis.

ABNA24 : A wata zantawa da ya yi da tashar talabijin ta Almayadeen a daren jiya, dangane da cikar shekara guda da kisan babban kwamandan sojin Iran Qassem Sulaimani da abokinsa kuma mataimakin kwamandan dakarun Hashd Sha’abi Abu Mahdi Almuhandis, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya tabo batutuwa da dama da suka shafi wannan batu, da ma wasu batutuwan da suka shafi siyasar yankin gabas ta tsakiya.

Da farko dai ya fara ne da bayyana irin gagarumar gudunmawar da Qassem Sulaimani ya bayar wajen tunkarar shirin Amurka da Isra’ila ‘yan korensu wajen rusa wasu kasashen musulmi da na larabawa a yankin gabas ta tsakiya, musamman a kasashen Lebanon, Syria, Iraki da kuma Falastinu.

Nasrullah ya ce Qassem Sulaimani ya bayar da gudunmawa babba wajen fatattakar Isra’ila a lokacin da ta kaddamar da yaki kan kasar Lebanon a shekara ta 2006, kamar yadda kuma dama tun tsawon shekaru shi ne gishikin taimakawa kungiyoyin Falastinawa wajen tunkarar Isra’ila musamman a Zirin Gaza, kamar yadda kuma ya gudunmawar da ya bayar a Syria da Iraki wajen yaki da ‘yan ta’addan Daesh ba a boye take ga kowa a duniya ba.

Dangane da wata tafiya da Qassem Sulaimani ya yi zuwa kasar Rasha a shekarun baya kuwa, Nasrullah ya bayyana cewa, Qassem Sulaimani ya gana da shugaba Putin tsawon sa’oi biyua jere, inda ya gamasar da Putin kan muhimmancin shigar Rasha a cikin yakin da manyan kasashen duniya da wasu gwamnatocin larabawa suka kaddamar a kan Syria da nufin rusa ta, inda sakamakon haka ne Rasha ta tura sojoji mayaka domin yaki da ‘yan ta’adda da kasashen duniya ke amfani da domin rusa kasar Syria.

Ya ce tun kafin wannan lokacin Amurka da Isra’ila da wasu ‘yan korensu a cikin kasashen larabawa suna da shirin yin kisan gilla a kan Qassem Sulaimani, amma ba su samu sa’ar hakan ba saia shekarar da ta gabata, kasantuwar ya zama babban karfe kafa da ke kawo cikas ga manufofin Amurka da Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.

342/