Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

27 Disamba 2020

12:45:42
1100096

Shekara 1 Da Shahadar Qassem Sulaimani Da Abu Mahdi Almuhandis

Ma’ikatar raya al’adu ta kasar Iran ta sanar da cewa, ofishinta da ke birnin Beirut na kasar Lebanon zai jagoranci gudanar da zaman taro, wanda zai yi dubi kan cikar shekara guda da shahadar manyan kwamandoji biyu, Qassem Sulamani da kuma Abu Mahdi Almuhandis.

ABNA24 : Wannan taro dai zai kunshi manyan malamai da kuma masana gami da wakilan kungyoyi daban-daban a kasar Lebanon, daga ciki har da wakilan kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa.

Babbar manufar wannan taro dai shi ne ci gaba da raya tafarkin wadannan manyan kwamandoji biyu da su ka yi shahada wajen kare martabar addini, daga yunkurin makiya na bata sunan addinin muslucni ta hanyar kirkiro ‘yan ta’adda masu kisan bil adama da sunan addini ko jihadi.

A shekarar da ta gabata ce Amurka bisa umarnin shugaban kasar ta kai hari da jirgi maras matuki a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagadaza, inda ta kashe Qassem Sulaimani babban kwamandan dakarun Quds a Iran, da kuma Abu Mahdi Almuhandis mataimakin babban kwamandan dakarun Hash Al-shaabi na Iraki.

342/