Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

5 Oktoba 2020

11:43:35
1075911

Mabiya Mazhabar Iyalan Gidan Manzon Allah (S) Sun Fara Tururuwa Zuwa Karbala Don Juyayin 40

Dubban mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (s) daga kasashen duniya da dama da kuma cikin kasar ta Iraki sun fara tururuwa zuwa birnin Karbala na kasar don halartar juyayin 40 na shahadar Imam Husain (a) jikan manzon Allah (s).

ABNA24 : A cikin watan Augusta ne aka gudanar da juyayin ranar shahadarsa da sahabbansa a Karbala wanda ya kasance ranar 10 ga watan Muharram.

A wannan shekarar dai gwamnatin kasar Iraqi ta takaida yawan masu ziyara zuwa birnin na Karbala saboda hana yaduwar cutar korona a kasar.

Gwamnatin kasar ya zuwa yanzu ta bukaci ko wace kasa ta aiko da masu juyayi 1,500 kacal. Sai kasar Iran wacce aka bukaceta ta aiko masu ziyara 2,500.

Ya zuwa yanzu dai mutane 375,000 ne suka kamu da cutar Korona a kasar Iraqi tare da mutuwar mutane 9500 daga cikinsu.

A wannan karon dai an dauki matakan tsaron da aka saba da kuma matakan kare mutane daga harbuwa da cutar ta korona.

342/