Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

19 Yuli 2020

13:48:01
1056146

​Lauyoyin Sheikh Zakzaky Sun Bukaci A Sake Shi Tare Da Mai Dakinsa

<p "="">Lauyoyin sheikh Ibrahim Zakzaky Jagoran Harka Islamiyya a Najeriya, sun bukaci da a sake shi tare da mai dakinsa da ake tsare das u, sakamakon matsalolin da suke fama da su.

ABNA24: A wata zantawa da ya yi da tashar press tv, Mas’ud Shajareh shugaban kwamitin kare hakkokin musulmi a kasar Burtaiya ya bayyana cewa, lauyoyin sheikh Ibrahim Zakzaky sun bukaci da a sake da mai dakinsa sakamakon matsalolin da suke fama da su na rashin lafiya.

Shajare ya ci gaba da cewa, ya zanta da lauyin da suke kare sheikh Zakzaky da mai dakinsa, inda suka sheda masa cewa sun bukaci kotu da ta sake su, kasantuwar suna da rashin lafiya, ga kuma halin da ake ciki na cutar corona.

Ya ce tun bayan kama shi a karshen shekara ta 2015, a cikin shekara ta 2016 kotu ta bayar da umarnin a saki Sheikh Zakzaky tare da maidakinsa malama Zinat har ma da biyansu tara ta kudi, umarnin da har yanzu ba a aiwatar ba.

Haka nan kuma ya kara da cewa, yanzu haka an sanya ranar 30 ga watan Yuli da muke ciki ta zama ranar sauraren bahasi kan batun da lauyoyin suka gabatar na neman a saki shi da maidakinsa.

342/