Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa TV
Asabar

23 Mayu 2020

06:36:22
1039516

Kasashen Turai Sun Ja Kunnen Isra’ila Kan Mamayar Falasdinu

Jami’an diflomatsiyan turai a kwamitin tsaro na MDD, sun bukaci sabuwar gwamnatin Isra’ila, da ta dakatar da shirinta na mamaye wasu yankunan Falasdinawa.

(ABNA24.com) Jami’an diflomatsiyan turai a kwamitin tsaro na MDD, sun bukaci sabuwar gwamnatin Isra’ila, da ta dakatar da shirinta na mamaye wasu yankunan Falasdinawa.

Jami’an kasashen da suka hada dana Estonia, Jamus, Belgium, Faransa da Poland, sun bayyana shirin na Isra’ila a matsayin wanda ke keta dokokin kasa da kasa, kamar yadda yarjejeniyar da aka shata a shekara 1967 ta tanada.

Kasashen turan sun sha alwashin daukar matakin takunkumi kan duk wani yunkurin Isra’ilar na ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawan.

Wasu daga cikin jami’an diflomatsiyyan sun ce duk wata mamayar Falasdinu, ko da tare da goyan bayan Amurka ne, zata tilasta wa kwamitin tsaron MDD, daukan mataki ta hanyar gabatar da kudiri.

Da yake karin haske kan batun, ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean Yves Le Drian, ya ce tini suka fara tattaunawa da wasu kasashen larabawa musamman Masar da Jordan, wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila, domin su ma su isar da sakon ga gwamnatin Isra’ilar.

Kafin hakan dai shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya bayyana aniyar Falasdinawa ta yin fatali da duk wasu yarjeniyoyi da fahimta da suka cimma da Isra'ila da Amurka, domin nuna adawa da shirin Isra'ilar na mamaye wasu yankuna a yammacin kogin Jordan.

Matakin na Abbas na zuwa ne, don mayar da martani kan shirin da firaministan Isra'ila ya ayyana na mamaye wasu sassan yammacin kogin Jordan da amfani da dokar Isra'ila kan matsugunan da Isra'ilan ta gina, yayin da majalisar dokokin kasar ta rantsar da sabuwar gwamnatinsa a ranar Lahadi.


/129