Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa TV
Asabar

23 Mayu 2020

06:36:22
1039515

Iran: Ranar Quds Ranar Hadin Kan Al’ummar Musulmi Ce

A cikin wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da dangane da ranar Quds ta duniya, ta bayyana wannan rana a matsayin ranar da take hada kan musulmi a kan batun Falastinu.

(ABNA24.com) A cikin wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da dangane da ranar Quds ta duniya, ta bayyana wannan rana a matsayin ranar da take hada kan musulmi a kan batun Falastinu.

Shafin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya saka bayanin da ma’aikatar ta fitar, wanda take jaddada muhimmancin da ke tattare da wannan rana ta Quds ta duniya, wadda take a matsayin wani babban lamari da ke hada al’ummar musulmi domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da ke karkashin zalunci da mamaya.

Bayanin ya ce; a kowace shekara ana gudanar da taruka da kuma jerin gwano da rubutun makaloli a kan sha’anin Falastinu da kuma mamayar da yahudawa suke yi wa yankunan Falastinun, da hakan ya hada har da masallacin Quds.

Babbar manufar hakan dai ita ce nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu, tare da karfafa gwiwarsu, da kuma kara tabbatar musu da cewa, al’ummomin duniya masu ‘yanci suna tare da su, tare da jaddada wajabcin ganin an kawo karshen mamayar yankunan Falastinawa.

Bisa ga al’ada dai a ranar Quds ta duniya ana gudanar da jerin gwano ne a fadin kasar Iran, amma a bana sakamakon bullar cutar corona, hakan yasa an takaita tarukan a masallatai da kuma cibiyoyin ilimi a biranan da ba su fuskantar wata barazana ta a zo gani dangane da cutar corona.


/129