Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci
Asabar

9 Mayu 2020

05:18:31
1034794

Muna taya Al’umma murnar ranar haihuwar Imam Hassan Al-Mujtabah[AS]

Muna taya daukakin al’ummar musulmi murnar tunawa da ranar da aka haifi limami na biyu cikin jerin limaman shiriya na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Hassan Al-Mujtabah[AS].

(ABNA24.com) - Muna taya daukakin al’ummar musulmi murnar tunawa da ranar da aka haifi limami na biyu cikin jerin limaman shiriya na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Hassan Al-Mujtabah[AS].

Shi dai Imam Hassan dan Sayyida Fatimah Azzahra ne, mahaifin sa kuma shine Sayyiudul Ausiyaa Imam Ali [AS]. An haifi Imam Hassan [AS] ne a ranar 15 ga watan ramdan shekara ta 3 bayan hijirar Manzon Allah[SAWA] a birnin madina.

Ya rayu gaba daya a duniya tsawon shekaru 47 amma ya jagoranci al’umma ne tsawon shekaru 10.

Muna jadda taya murna ga daukakin al’umma musamman ma mabiya Ahlul Bait[AS] murnar tunawa da ranar haihuwar Imam hassan[AS].


/129