Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Litinin

17 Faburairu 2020

10:05:15
1011087

Rouhani: Amurka Ta Gaza Wajen Cimma Manufarta Na Matsin Lamba Kan Iran

Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar tuni siyasar matsin lamba na ƙoli da Amurka take gudanarwa kan ƙasar Iran ya ci ƙasa don kuwa dukkanin alƙalumman da bincike na tattalin arziki sun nuna cewa Amurka ba ta cimma wannan manufa na ta ba.

(ABNA24.com) Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar tuni siyasar matsin lamba na ƙoli da Amurka take gudanarwa kan ƙasar Iran ya ci ƙasa don kuwa dukkanin alƙalumman da bincike na tattalin arziki sun nuna cewa Amurka ba ta cimma wannan manufa na ta ba.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai na ciki da wajen ƙasar Iran inda yace dukkanin alƙalumma da bayanan masanan tattalin arziki sun bayyana cewar tuni Iran ta tsallake dukkanin fagagen tsanani na wannan matsin lambar.

Shugaban na Iran ya ce a halin yanzu Amurkawan sun gane cewa tunanin da suke yi na cewa matsin lambar tattalin arzikin da suke yi wa Iran zai tilasta mata zama teburin tattaunawa da su cikin ƙasƙanci wani lamari ne ba mai yiyuwa ba.

Yayin da yake amsa tambaya dangane da zaɓen shugaban Amurka da za a gudanar a nan gaba kuwa da kuma ƙoƙarin shugaban Amurkan Donald Trump na ci gaba da shugabancin Amurkan, shugaban Rouhani ya ce Iran ba ta damu kowace jam’iyya ce za ta ci zaɓe a Amurkan ba, wannan ba shi da muhimmanci a wajen Iran, abin da ke da muhimmanci shi ne manufar ƙasar Iran da kuma yadda za ta cimma waɗannan manufar.



/129