Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Litinin

17 Faburairu 2020

10:05:14
1011085

Iran Ta Karyata Kwace Makamanta Da Amurka Ta Ce Ta Yi A Takun Aden

Wani kwamanda na dakarun kare juyin musulunci na Iran ne ya yi watsi da riyawar da Amurka ta yi na cewa ta kwace makaman Iran da su ke kan hanyar zuwa kasar Yemen, akan tekun Aden.

(ABNA24.com) Wani kwamanda na dakarun kare juyin musulunci na Iran ne ya yi watsi da riyawar da Amurka ta yi na cewa ta kwace makaman Iran da su ke kan hanyar zuwa kasar Yemen, akan tekun Aden.

Real Admiral Ali Fadawi ya kara da cewa; Amurkan ta bayyana hakan ne domin ta rufe kashin da ta ke sha a kasar Yemen, kuma daga lokaci zuwa lokaci tana fadin hakan domin ta samarwa kanta dalilin cin kasa a Yemen.

Fadawi ya kara da cewa; Abu ne mai yiyuwa al’ummar Yemen su sayo makamai daga wata kasa, wanda hakan hakkinsu ne, don haka yin zargi irin wannan abin kunya ne ga Washington.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Amurkan ta riya cewa sojojin ruwanta sun kwace makamai kirar Iran da su ke kan hanyarsu zuwa kasar Yemen, da su ka hada da na harbo jiragen sama da kuma tankokin yaki.




/129