Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Litinin

17 Faburairu 2020

10:05:14
1011084

Dr. Ali Larijani Ya Bayyana Kasar Syria A Matsayin Mai Muhimmanci A Tsakanin Kasashen Gwagwarmaya

Kakakin majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani wanda ya ke ziyarar aiki a kasar Syria, ya bayyana muhimmancin alaka ta ‘yan’uwantaka da ke tsakaninta da Iran, sannan ya kara da cewa; Tana da matukar muhimmanci a tsakanin kasashen gwagwarmaya.

(ABNA24.com) Kakakin majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani wanda ya ke ziyarar aiki a kasar Syria, ya bayyana muhimmancin alaka ta ‘yan’uwantaka da ke tsakaninta da Iran, sannan ya kara da cewa; Tana da matukar muhimmanci a tsakanin kasashen gwagwarmaya.

Dr. Larijani ya kara da cewa; Za mu gudanar da shawarwari akan batutuwan da su ke faruwa a cikin wannan yankin,haka nan kuma alakar da ta ke tsakanin kasashen biyu

Kamfanin dillancin labarun kasar Syria “ SANA” ya bayar da labarin cewa shugaban majalisar ta Iran ya sami tarbar takwaransa na Syria, Hammoudah, Sabbagh.

A yau Lahadi ne dai shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran din ya isa kasar Syria tare da babbar tawaga da ta ke rufa masa baya.




/129