(ABNA24.com) Wata sanarwa da ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, cewa da (Ocha) ta ce fararen hula 31 ne suka rasa rayukansu kana wasu 12 suka jikkata a harin saman da aka kai yankin Al-Jawf a jiya Asabar.
Harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da ‘yan Houtsis suka sanar da kakkabo wani jirgin sojin kawancen a ranar Juma’a.
A watan Maris na shekara 2015 ne Saudiyya da kawayenta suka kaddamar da yaki kan ‘yan Houstis na Yemen dake yaki da zalinci da danniya a kasar, lamarin da ya jefa kasar cikin hali mafi muni a duniya a cewar MDD.
Alkalumman da MDD, ta fitar sun kiyasta kasha 80 cikin dari na al’ummar kasar ta Yemen kwatancin mutane miliyan 24 na bukatar tallafin gaggawa.
/129
Madogara : Husa TV
Litinin
17 Faburairu 2020
10:05:14
1011083
Harin Saudiyya Ya Kashe Fararen Hula 31 A Yemen
MDD, ta bayyana cewa akalla fafaren hula 31 ne suka rasa rayukansu a wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai a kasar Yemen.