Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Pars Today
Asabar

8 Faburairu 2020

10:20:18
1008581

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dau mataki na shari'a a kan shugaban kasar Amurka, Donald Trump saboda ayyukan ta'addanci na tattalin arziki, soji da kuma na al'adu a kan kasar.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dau mataki na shari'a a kan shugaban kasar Amurka, Donald Trump saboda ayyukan ta'addanci na tattalin arziki, soji da kuma na al'adu a kan kasar.

Mr. Zarif ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Labanon inda ya ce: Ko shakka babu Iran za ta dau mataki na shari'a a kan Trump bisa laifuffuka guda uku da suka hada da ta'addanci na tattalin arziki sakamakon irin takunkumin zaluncin da yake ci gaba da sanya wa Iran da kuma laifin ta'addanci na soji da na al'adu bisa kisan gillan da suka yi wa Laftanar Janar Qasim Soleimani bisa umurnin Trump a ranar 3 ga watan Janairun da ya gabata da kuma barazanar da Trump din yayi na kai hari kan cibiyoyi na al'adu da tarihi na Iran.

A kwanakin baya ne dai Trump din yayi barazanar kai hari kan cibiyoyi da wuraren tarihi na Iran matukar dai Iran din ta mayar da martani ga kisan gillan da Amurka ta yi wa Janar Qasim Soleimanin lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniya.

A wani bangare na hirar, ministan harkokin wajen na Iran yayi watsi da shirin Amurka na 'sulhu' tsakanin Palastinawa da Isra'ila da suka kira shi da 'Mu'amalar Karni' yana mai cewa Trump ya ma fi sahyniyawan wuce gona da iri kan Palastinawan yana mai cewa wannan shirin na su babu inda zai je don kuwa dukkanin kungiyoyin Palastinawa din ma sun yi watsi da shi.