Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Asabar

8 Faburairu 2020

10:18:56
1008580

Wanda Ya jagoranci Sallar Juma’a A Tehran Ya Ce: Yarjejeniyar Karni Ta Kunyata Amurka

Wanda ya jagoranci sallar juma’a anan Tehran ya bayyana cewa; Yarjejeniyar karnin, abin kunya ne na karni, kuma abin da Amurkan ta yi, tamkar kwancewa kanta zane ne a cikin kasuwa.

(ABNA24.com) Wanda ya jagoranci sallar juma’a anan Tehran ya bayyana cewa; Yarjejeniyar karnin, abin kunya ne na karni, kuma abin da Amurkan ta yi, tamkar kwancewa kanta zane ne a cikin kasuwa.

Ayatullah Imami Kashani ya kuma bayyana cewa; “Yan sahayoniya barayi ne da su ke kwace gidajen Palasdinawa sannan kuma suna kokarin halartawa kansu yin hakan ta hanyar abinda aka kira : “ Yarjejeniyar karni.”

Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa; Babu inda yarjejeniyar karni za ta je, za ta rushe.

Da yake Magana akan zagayowar ranakun cin nasarar juyin musulunci na Iran, Ayautullah Muhammad Imami Kashani ya ce; Ba domin nasarar da juyin musulunci a Iran ya samu ba, to da tuni Amurka da HKI sun shimfida ikonsu a duniyar musulmi baki daya.

Limamin na Tehran ya kuma juyin musulunci na 11 ga watan Febrairu 1979, wani gagarumin sauyi ne da ya faru a tarihi, domin kai wa ga cimma manufofin annabawan Allah da waliyan Allah.



/129